Ba na zargin Southgate kan raunin Lallana -Jurgen Klopp

Kociyan Liverpool Jurgen Klopp Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kociyan Liverpool Jurgen Klopp ya ce ba ya zargin kocin Ingila Gareth Southgate,

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce ba ya zargin kocin Ingila Gareth Southgate kan raunin da Adam Lallana ya samu, sai dai bai ji dadin yadda dan wasan gaban ya buga manyan wasannin biyu ba.

Lallana, mai shekara 28 ya samu raunin ne, a cinyarsa lokacin da Ingila ta samu nasara a kan Lithuania a wasan neman gurbin kofin duniya a ranar Lahadin da ta gabata, bayan sun buga wasan sada zumunci da Jamus ranar 22 ga watan Maris.

Zai yi jinyar wata guda, hakan na nufin kenan ba zai buga wasansu da Everton ba a ranar Asabar, wanda wasa ne mai zafi.

Kocin dan kasar Jamus ya ce, "Ban ji dadin wasan da ya buga a ranar Laraba ba, amma ba wai ina zargin Gareth Southgates ba ne."

"Ina tunanin dama dole a samu yarjejeniya da kocin kulob din kasa. Ba wai muna yaba kiran da ya yi masa ba ne, dama abu ne da aka saba yi. 'Yan wasan duka namu ne.

"Ina girmama hukuncin da sauran manajoji suke dauka 100 bis 100, saboda su ma dole su girmama hukuncina."

Lallana dai ya buga wasan sama da sa'a guda a wasan sada zumunci da Ingila ta buga da Jamus a birnin Dortmund, wasan da ya zo kasa da sa'o'i 72 bayan da Liverpool din ta kara da Manchester City a gasar Firimiya, kafin kuma daga baya ya buga wasan minti 90 da kasar ta buga da Lithuania.

Amma Klopp na ganin cewa ya kamata hukumar FA ta rika aiki tare da ta Firimiya da kungiyoyin da manema labarai saboda kyakkyawan tsarin wasannin Ingila.

"Hakika ina ganin cewa za mu tafiyar da al'amuran daidai idan muka yi aiki tare," in ji shi.

"In dai ba za mu rika aiki tare ba to lallai irin wadannan abubuwa za su rika faruwa ko yaushe."

Labarai masu alaka