Crystal Palace na son tsawaita zaman Zaha a kungiyar

Wilfried Zaha Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Zaha ya ci kwallo a karawar da Palace ta doke Chelsea

Shugaban kungiyar Crystal Palace Steve Parish, na shirya wata tattaunawa da za ta tsawaita zaman dan wasan gefen kungiyar Wilfried Zaha, idan kungiyar ta ci gaba da buga gasar Premier.

Zaha, mai shekara 24 ya kulla kwantiragin shekara biyar da rabi da kungiyar, lokacin da ya zo daga Manchester United a watan Fabrairun 2015.

Ya zura kwallon da ta bai wa kungiyar nasara a kan Chelsea, wacce ke kan gaba a kan tebur a karawar da suka yi ranar Asabar, wanda hakan ya ba su ratar maki hudu daga rukunin masu faduwa daga gasar.

Parish ya fada a wani gidan radiyon BBC cewa, "Muna son dan wasan, za mu yi magana da shi muddin dai muka tsira."

Zaha dai ya nemi amincewar kasa-da-kasa domin komawa kasar Ivory Coast daga Ingila, kuma ya buga gasar kasashen Afirka ta 2017.

Sai dai wakilin dan wasan ya ce,Tottenham ta taya dan wasan kan fam miliyan 15 a kakar sayar da 'yan wasa da ta wuce.

Labarai masu alaka