Luke Shaw na da jan aiki a gabansa — Mourinho

Luke Shaw Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shaw ya zo United ne daga Southampton a watan Yuni 2014 a kan fam miliyan 27

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya nuna rashin gamsuwa da rawar da Luke Shaw ke taka wa a kulob din.

Dan wasan mai shekara 21 ya buga wasa 15 ne kacal a kakar bana kuma rabonsa da wasa tun lokacin da United ta tashi 1-1 da Bournemouth.

Hakan ne ya sa Mourinho ya ce dan kwallon ba ya taka rawa kamar sauran 'yan baya irin su Ashley Young da Matteo Darmian da Daley Blind.

Ya ce, "Ba zan iya kwatanta yadda yake atisaye ba, don hazakarsa ba ta kai ta sauran ba. Yana da jan aiki a gabansa."

An tambayi Mourinho ko yana hasashen dan wasan na Ingila ya taka rawar da ta fi wannan, sai ya ce, "Joe Hart ma dan wasan Ingila ne kuma ga shi nan yana taka rawa a matsayin aro a Italiya."

A shekarar 2014 ne Shaw ya koma United a kan kudin fam miliyan 27, amma ya samu karaya a kafarsa a watan Satumbar 2015, abin da ya hana shi buga wasa na tsawon shekara biyu.

Labarai masu alaka