Arsene Wenger ya yabi magoya bayan Arsenal

Magoya bayan kulob din Arsenal Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Magoya bayan Arsenal sun yi zanga-zanga a filin wasan Emirates

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger, ya ce magoya bayansu sun cancanci yabo, bayan karawarsu da Manchester City, inda suka ta shi kunnen doki, da ci 2-2, duk kuwa da kiran da suka yi cewa ya yi murabus.

Wannan yabo daga Mista Wenger na zuwa ne duk da zanga-zangar da magoya bayan Arsenal din suka yi a filin wasa na Emirates.

Wenger da yanzu ke cikin tsaka mai wuya, inda magoya bayan ke kiran sa da ya yi murabus, bayan nasarar wasa daya tilo cikin wasanni shida da kulob din ya buga, kazalika kuma ya kara yin kasa a teburin jadawalin gasar Premier.

"A gaskia duk da yadda lamarin ya kasance, magoya bayanmu sun yi kokari yau" In ji kociyan, wanda asali dan Faransa ne.

Sau biyu dai Arsenal din na farke cin da kulob din Man. City ya yi masu, inda aka tashi wasan da ci 2-2.

Labarai masu alaka