Rauni zai iya hana Sadio Mane buga Premier

Dan wasan gaban Liverpool Sadio Mane Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dan wasan gaban Liverpool Sadio Mane, ya samu rauni a gwiwarsa, wanda ka iya hana shi buga wasannin Premier

Dan wasan Liverpool Sadio Mane ba zai buga wasan da zasu kara da Bournemouth ranar Laraba, amma Jurgen Klopp ya ce akwai yiwuwar dan wasan gaban ba zai buga sauran wasannin kakar gasar Premier bana ba.

Mane mai shekaru 24 ya samu rauni ne a gwiwar sa ranar Asabar da suka gabata, a wasan da Liverpool din ta buga da Everton, inda suka lallasa su da ci 3-1 a gidansu.

Rahotanni sun ce akwai Mane, wanda aka saya da kudi fan miliyan 34 daga Southampton a bazarar bara, ba zai buga sauran wasannin gasar ba.

"Ba a dai tabbatar dari bisa dari ba. Za mu jira mu gani dai."In ji kociyan Liverpool Klopp.

Labarai masu alaka