Conte na iya zama kocin da ya fi ko wanne a duniya — Guardiola

Antonio Conte and Pep Guardiola Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Chelsea ta samu nasara a kan Manchester City da ci 3-1 a watan Disamban bara

Kocin kulob ɗin Chelsea Antonio Conte zai iya zama "kocin da ya fi ƙwarewa a duniya, kuma na koyi abubuwa da yawa daga Chelsea ƙarƙashin jagorancinsa,"kamar yadda kocin Manchester City Pep Guardiola ya bayyana.

Wannan ce kakar wasa ta farko da Guardiola da Conte suka fara aiki a Ingila kuma za su fafata a ranar Laraba.

Conte ya samu nasarori da dama, inda Chelsea take ci gaba da jagoranci a Gasar Firimiya, yayin da ta bai wa Manchester City, wadda take mataki na huɗu, tazarar maki 11.

"Ra'ayina game da abokin aikina Conte shi ne cewa lallai shi ƙwararre ne," inji Guardiola.

Ya ƙara da cewa: "Ya sa tawagar Italiya ta buga wasanni masu ƙayatarwa, hakazalika kulob ɗin Juventus. Koci ne da ya ƙware, na koyi abubuwa a duk lokacin da nake kallon wasan yaransa a Juventus da Italiya da kuma yanzu. Duk kulob ɗin da yake horarwa suna samun ƙwarewa ta fuskoki da dama. Wataƙila shi ne yake da ƙwarewar."

Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Wannan ne kakar wasa na farko da Guardiola ya gaza ciyowa kulob ɗinsa kofi

Guardiola ya karbi ragamar jagorancin Manchester City ne a bara bayan ya jagoranci Bayern Munich, wadda ta samu nasara a Gasar Bundesliga har sau uku a jere da kuma gasar Geman Cup sau biyu a shekarar 2013 da kuma 2016.

Gabanin haka, kocin ya jagoranci Barcelona ta samu nasara a gasar La Liga har sau uku, da gasar Copa del Reys da kuma gasar Zakarun Turai, kuma ya ci kofi biyu a ko wacce.

Sai dai kocin mai shekara 46 ya sha faɗin cewa hakar Manchester City za ta cimma ruwa a ƙarƙashin jagorancinsa.

"Ya kamata na ciyo kofi uku kuma na sauya wasan ƙwallon ƙafa a Ingila. An sa buri sosai a kaina, saboda haka wajibi ne na kasa kai wa matakin da aka tsammace ni na kai. Sai dai ba zan iya yin nasara ba a kakar bana," inji Guardiola.

Ya ci gaba da cewa, "A Barcelona mun ciyo kofi uku a jere, mun buga duka wasanninmu a gasar da muke ciki, mun buga gasar Zakarun Turai duk bayan kwana uku, kuma mun buga ba tare da bata lokaci ba. A wasu lokuta kana buƙatar ƙarin lokaci."

Chelsea ta sha kashi a gida a hannun Crystal Palace a ƙarshen makon jiya, sai dai ga alama hakan bai ba Guardiolan ƙwarin gwiwa ba, gabanin karawarsa da Chelsea ranar Laraba, wadda ta jera wasa 10 a gida ba tare da rashin nasara ba, gabanin wasansu da Palace.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba