"Shaw ya yi amfani da kwakwalwata ne" Mourinho

Mai tsaron gidan Manchester United, Luke Shaw Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mourinho ya ce Luke Shaw na gabansa, kuma shi ne ya ke gaya masa abin da zai yi

Jose Mourinho ya ce Luke Shaw ya yi amfani da jikin sa ne amma da kwakwalwar shi Mourinho a yayin wasan da Manchester ta buga da Everton, da suka tashi kunnen doki, inda ya kara jaddawa 'yan wasan kulob din da cewa suna bukatar saurin girma.

Mai tsaron gida Shaw, da ke da shekaru 21 ya fito fili ne a daren ranar Talata, tun watan Junairu, kuma kwallon da ya buga ne a daidai karin lokacin bayan wasa ne ya yi sanadin bugun fenaritin da ya sa Zlatan Ibrahimvic ya daidata sahun cin.

"A daidai gaba na ya ke, kuma ni na ke ba shi shawarar abin da zai yi." In ji Mourinho.

Ya kuma kara da cewa, "Dole ne ya sauya tunanin da ya ke yiwa kwallo a kwakwalwarsa."

A ranar Litinin ma Mourinho ya sa alamar tambaya game da yadda Shaw ke mayar da hankali kan wasa.