An nada Paul Warne kociyan Rotherham United

Paul Warne, kociyan Rotherham United Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An nada Paul Warne a matsayin kociyan Rotherham United

Kulob din da aka fitar daga rukunin gasar Championship, Rotherham United ta nada shugaba mai rikon kwarya Paul Warne, a matsayin kociya, bisa yarjejeniyar shekara daya.

Tsohon dan wasan tsakiyan Rotherham din, mai shekaru 43, ya karbi ragamar na rikon kwarya a watan Nuwambar bara, bayan da tsohon jagoran Kenny Jackett ya yi murabus.

An fitar da su a rukunin farko ne da wasu, bayan shan da Fulham ta yi masu ranar Asabar, duk da wasannin bakwai da ke gaban su.

Shugaban kungiyar Tony Stewart, ya ce,"Paul na sane da cewa kulob din na bukatar gyara. Dama shi dan Miller ne gaba da baya."