Yakubu Ayegbeni da Coventry sun raba gari

Yakubu Ayegbeni Hakkin mallakar hoto Getty Images

Dan wasan Conventry Yakubu Ayegbeni ya kawo karshen kwantiraginsa da kulob din.

Tun da farko kwantiragin dan wasan mai shekara 34 ya kamata ya kai har karshen kakar wasanni na watan Fabrairu.

Kulob din nasa ne dai ya sanar da cewa za a yanke yarjejeniyar nan take.

Yakubu ya fito a wasa uku ne kawai, inda daga nan ya samu rauni a bayan cinyarsa, a yayin karawarsu da Swindon Town.

Kulob din ya ce yana yi wa Yakubu fatan alkhairi.

Labarai masu alaka