Ina nan daram a Chelsea — Conte

Antonio Conte Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Ina nan daram a Chelsea: Conte

Kocin Chelsea Antonio Conte ya nanata sha'awarsa ta ci gaba da zama a Chelsea, duk da rade-radin da ke cewa zai koma Italiya.

An yi ta rade-radin cewa tsohon kocin Italiya da Juventus din, zai koma kungiyar Inter Milan.

Conte, mai shekara 47, wanda ya sanya hannu a kwantiragin shekara uku da Chelsea a bara, ya shaida wa kafar yada labarai ta Sky Sport Italia cewa "yanzu muna cikin wani yaki."

"Muna son kammala wannan kakar, da samun wani gagarumin abu da ba a tsammani. Sannan sai mu yi kokarin gina wani babban abu gaba-daya."

Cheasea dai na mataki na daya a gasar Firimiya da tazarar maki bakwai tsakaninta da Tottenham wacce ke mataki na biyu, yayin da ya rage wasanni takwas a kammala gasar.

Labarai masu alaka