Lingard zai karɓi maƙudan kuɗaɗe a United

Lingard ( a tsakiya) lokacin da suke murnar lashe kofin gasar lig ta Ingila bayan sun doke Southampton a watan Fabrairu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Lingard ( a tsakiya) lokacin da suke murnar lashe kofin gasar lig ta Ingila bayan sun doke Southampton a watan Fabrairu

Dan wasan tsakiya na Manchester United, Jesse Lingard na dab da kulla wata doguwar yarjejeniya a Old Trafford.

Dan wasan na Ingila mai shekara 24, yana magana da kungiyar a wadannan makonni a wata yarjejeniyar da za ta kai shi ga samun £100,000 a mako guda.

Lingard ya je United ne tun yana dan shekara takwas, kuma ya yi wa kungiyar wasanni 70.

Ya samu nasarar cin kwallo a wasanni uku da kungiyar da samu nasara a Wembley.

Bayan cin kwallon da ta ba wa kungiyar nasara a wasan karshe na kofin FA a Wembley, a kakar wasa da ta gabata, haka kuma ya ci kwallo a wasansu da Leicester a gasar Community Shield, sannan ya ci Southampton lokacin da United din ta ci kofin EFL a watan Fabrairu.

Lingard ya yi zaman aro a kungiyoyin Leicester, da Birmingham, da kuma Brighton, kafin Louis van Gaal ya sa shi a kakar wasansa ta farko da kungiyar ta kara da Swansea, a wasan farko na kakar 2014-15.

A kakar bana ya ci kwallo biyar, a wasanni 29 da ya buga karkashin koci Jose Mourinho.