Alexis Sanchez na son ci gaba da zama a Arsenal — Arsene Wenger

Alexis Sanchez Hakkin mallakar hoto Empics
Image caption Alexis Sanchez ya koma Arsenal daga Barcelona a 2014

Kocin Arsenal Arsene Wenger, ya ce dan wasan gaba na kungiyar Alexis Sanchez zai ci gaba da zama a kungiyar idan aka cimma wasu yarjejeniyoyi.

Dan wasan mai shekara 28, ya karbi kwantiragi ne da kungiyar har zuwa kakar bazarar 2018, sai dai wasu Jaridu na cewa zai so komawa Chelsea.

Wenger ya ce, "Na yi amanna yana son zama a kungiyar, kuma abu ne da zamu tattauna da wakilinsa."

Dan wasan dan kasar Chile, ya koma Arsenal ne daga Barcelona a kakar wasa ta 2014, a kan kudi pam miliyan 35, kuma ya ci wa Arsenal din kwallo 22 a kakar wasa ta bana.

Sai dai kuma, koma-bayan da Arsenal din ke samu a gasar Premier ta bana, da kuma ficewa daga gasar zakarun Turai tun a matakin kungiyoyi 16, rahotonni ke ta fitowa cewa dan wasan na duba yiwuwar barin Arsenal din.

A watan Maris, Wenger ya musanta cewa, ce-ce-ku-cen, da dan wasan ya yi da sauran 'yan wasan kungiyar a filin atisaye ne, ya sa bai sanya shi a wasan da kungiyar ta sha kaye a hannun Liverpool ba.

Wata daya bayan nan, Sanchez din ya mayar da martani game da rade-radin da wasu ke yi na cewa yana son koma wa Chelsea.

Wenger na magana ne a wajen wani taron manema labarai game da wasansu da Crystal Palace ranar Litinin mai zuwa, yayin da kocin dan Faransa, ya ki yin karin bayani game da makomarsa a kungiyar

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba