Cin kofin Turai ya fi kofin duniya wahala — Scott

'yan wasan Ingila mata Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tawagar mata ta Ingila na mataki na hudu a jadawalin da FIFA ta fitar a watan Maris

'Yar wasan baya ta Ingila da Alex Scott ta ce cin kofin Turai na mata ya fi wahala fiye da daukar kofin duniya.

A shirye-shiryen da Ingilan ke yi wa wasan na bana, wanda za a yi a kasar Netherlands, za ta karbi bakuncin Italiya a wasan sada zumunci ranar Juma'a a Vale Park.

Wasan shi ne na farko tun lokacin da koci Mark Sampson ya bayyana sunayen 'yan tawagar kasar 23 zuwa gasar ta Turai.

Scott ta shaidawa BBC Radio 5 live, cewa, "Mun yi amanna cewa za mu iya, amma ya kamata mu yi nasara a ko wanne wasanmu."

"Ba abu ne mai sauki ba. Ina ganin daukar kofin Turai ya fi wuya matuka a kan na kofin duniya," in ji ta.

Ta kara da cewa, "A gasar kofin duniya kana da salon wasanni mabambanta. Sau daya za ka kara da kowa, kuma abu ne mai sauki cin kwallo; amma a kofin Turai kowa sai ya ziyarci kowa."

Kalubalen dake gaban Lionesses

Kungiyar ta Lionesses za ta karbi bakuncin Austriya a filin wasa na Milton Keynes Don MK ranar Litinin, sai dai za su buga wasannin biyu ne, da tawagogi daban-daban, saboda Sampson din ya bayyana sunayen 'yan tawagar wasan Turai ta 2017 ne watanni uku kafin gasar ta fara.

'Yar wasan bayan ta Arsenal din Scott, na daya daga 'yan wasa hudu da ke cikin tawagar, wadanda ba za su buga wasanni biyu na sada zumunci ba, saboda murmurewa daga jinyar da suke yi.

Sauran su ne mai tsaron ragar Manchester City Karen Bardsley, da 'yar wasan Notts County Jo Potter, da kuma 'yar wasan gaba ta Chelsea Fran Kirby.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba