Man-City ta lallasa Hull City da ci 3-1

premier Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Sau daya kawai kulob din Hull City ya samu nasara a wasan waje a kakar bana

Kulob din Manchester City ya lallasa Hull City da ci 3-1 a fafatawar da suka yi ranar Asabar din nan a gasar Premier ta Ingila.

Dan wasan Hull City, Ahmed Elmohamady ne ya fara cin gida kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Raheem Sterling kuma ya gyara wa Sergio Aguero, wanda shi kuma ya jefa kwallo ta biyu cikin ragar Hull.

Fabian Delph ne ya ci kwallo ta uku daga tazara mai dan nisa.

Nasarar da Manchester City ta samu ta kawo karshen wasanni hudu da ta buga ba tare da ta ci kwallo ba.

Wannan nasara kuma ta sa yanzu kulob din yana da maki 61 a teburin Premier, inda kuma yake mataki na hudu.