An naushi dan wasan Everton a fuska

Everton

Wani faifan bidiyo da aka nada ta wata kyamarar CCTV kuma aka yada a kafafen sada zumunta, ya nuna yadda wani mutum ya rika kai wa dan wasan tsakiyar kulob din Everton, Ross Barkley, naushi a fuska.

Bidiyon ya nuna yadda wani mutum ya rika kai wa dan wasan naushi kafin daga bisani ya fadi a kasa.

Dan wasan mai shekara 23, bai ji wani mummunan rauni ba yayin lamarin, wanda ya faru sa'o'i kalilan bayan kammala wasan da ya taka leda, inda kulob dinsa ya samu nasara a kan Leicester City ranar Lahadi.

Sai dai kulob din Everton bai ce komai ba tukunna, kuma ba a shigar da kara ba a ofishin 'yan sanda game da batun.

"Ross bai takali wanda ya kai masa hari ba ranar Lahadi da yamma a birnin Liverpool," in ji Lauyansa Matt Himsworth.

Dan wasan kasar Ingilan wanda ya yi atisaye da takwarorinsa ranar Litinin, ya taba yi wa kasarsa wasa har sau 22, kuma yana cikin manyan 'yan wasan da kocin Ingila Gareth Southgate yake ji da su.

Dan wasan wanda aka haifa a birnin Liverpool, ya koma kulob din Everton ne yayin da yake da shekara 11 da haihuwa, kuma ya yi mata wasa har 173.

Labarai masu alaka