Sadio Mane ba zai yi wasa ba tsawon wata biyu

Sadio Mane Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mane ya ji cciwon ne sakamakon wani karo da suka yi Leighton Baines

Dan wasan gaba na kulob din Liverpool forward Sadio Mane, zai shafe wata biyu ba tare da ya yi wasa ba, sakamakon tiyatar da za a yi masa a gwiwarsa.

Ya ji rauni ne a gwiwarsa ta kafar hagu sakamakon karon da suka yi da Leighton Baines a wasan da suka ci Everton 3-1.

Koci Jurgen Kulopp ya ce, Mane dan shekara 25 yana bukatar a yi masa tiyata, "wanda hakan zai sa ba zai sake buga a wasa ba a wannan kakar wasannin."

Liverpool ce ta uku a teburin Premier, kuma tana da ragowar wasa shida.

Ana sa ran zai yi jinyar wata biyu bayan an yi masa tiyatar.

Mane ya koma kungiyar ne a akan fam miliyan 34 daga Southampton a bazarar bara, kuma da shi aka fara wasannin kungiyar in ban da guda shida na farko.

Daga cikin wasannin, sun yi nasara a daya, sun yi canjaras a guda uku yayin da aka ci su biyu.

Da yake magana gabannin nasarar da suka samu kan Stoke ranar Asabar, Klopp ya ce, "Shi ma Adama Lallana yana samun sauki, amma bai fara atisaye ba" don har yanzu bai gama warwarewa daga raunin da ya ji a cinya ba a watan Maris.

Ya kara da cewa, "Kyaftin Jordan Henderson ma wanda ba ya teka leda tun a watan Fabrairu, yana lafiya, amma ban san yaushe zai koma fagen atisaye ba."

Lokacin da Mane ya fara wasa da Liverpool Liverpool tsakanin 2016 zuwa 2017 Kafin Mane ya je Liverpool
26 Wasanni 6
17 Nasarori 1
6 Canjaras 3
3 Shan kaye 2
60 Kwallayen da suka ci 6
2.3 Kwallayen da suka ci a duk wasa 1
30 Kwallayen da aka ci su 8
1.2 Kwallayen da aka ci su a duk wasa 0.75
2.2 Makin da suka samu a duk wasa 1
Hakkin mallakar hoto @sadiomaneofficial
Image caption Sadio Mane ya wallafa wani hoto na raunin da ya ji a shafinsa na Instagram

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba