Arsene Wenger: Makomata ba ta shafar 'yan wasana

Arsene Wenger

Asalin hoton, Ashley Crowden - CameraSport

Bayanan hoto,

Crystal Palace ta doke Arsenal da ci 3-0

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce rashin tabbas game da makomarsa ba ta shafar yadda 'yan wasansa suke wasa, sai dai ya bayyana yadda suka sha kashi a hannun Crystal Palace ranar Litinin da "babban abin damuwa ".

Kwantaragin Wenger zai kare ne a karshen kakar bana kuma an ce za a sabunta shi zuwa shekara biyu, sai dai kocin bai bayyana ko zai ci gaba da zama a kulob din ba.

Arsenal tana mataki na shida ne, wato kawo yanzu sun gaza shiga jerin manyan kulob hudu da za su je Gasar Zakarun Turai, yayin da ya rage saura wasanni takwas a karkare Gasar Firimiyar bana.

"Na jagoranci Arsenal ta buga wasanni fiye da 1100 amma ba mu taba yi rashin nasara kamar yadda muke yi ba yanzu," inji Wenger.

Ya ci gaba da cewa "Sai mun yi wani abu cikin hanzari don ba za mu lamunci hakan ba."

Wasu magoya bayan kulob din sun shaida wa kocin cewa, "Lokacin tafiyarka ya yi", kuma suka rika rera wakoki suna cewa, "ba ka cancanci jagorancin" 'yan wasan Arsenal ba, saboda yadda Crystal Palace da ke gab da faduwa daga Gasar Firimiya ta doke su da ci 3-0.

Wasan ranar Litinin din shi ne na hudu a jere da Arsenal ta yi rashin nasara a waje, kuma wannan ne na farko a tsawon tarihin Wenger a kulob din.

Rashin nasarar kulob din ya sa da wuya su iya zuwa Gasar Zakarun Turai. Kuma wannan shi ne karon farko da hakan zai faru karkashin jagorancin kocin.

"Na fahimci yadda magoya bayanmu ba sa jin dadi, mu ma ba ma jin dadi kwarai da gaske," inji Wenger

Ya ci gaba da cewa: "Abin yana jawo damuwa kuma akwai takaici kan yadda muka yi rashin nasara a wasan. Palace suna da kwazo, sun taba samun nasara a kan Chelsea, wanda hakan yake nuni da yadda suke kankankan da juna."

"Muna cikin matsakaicin hali. Wasanmu na da daren Litinin bai taimake mu ba sam."