Tuggu aka shirya min na bar Leicester — Ranieri

Leicester City

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Claudio Ranieri ne ya jagoranci Leicester City ta yi nasarar lashe gasar Premier

Tsohon kocin Leicester Claudio Ranieri, ya yi amanna cewar wani ne a cikin kulob din ya shirya masa gadar zare, amma ba ya tunanin 'yan wasansa ne suka sa aka sallame shi daga kungiyar.

Mista Ranieri, dan Italiya ya yi sanadin da kolub din ya lashe gasar Premier a kakar wasannin da ta gabata, amma sai aka kore shi a watan Fabrairu.

Mista Ranieri ya shaida wa Sky Sports cewa, ''Ban yarda cewa 'yan wasana ne suka sa aka sallame ni ba, a'a-a'a.''

''Watakila dai wani ne yake yi min bi-ta-da-kulli. A shekarar da ta gabata matsalata karama ce, amma duk da hakan mun yi nasara a gasar.''

Ya kara da cewa, "Watakila da muka ja baya a bana, sai wasu mutanen suka shirya min gadar zare."

A lokacin da aka kori Mista Ranieri, maki daya ne ya sa ya tsira daga faduwa a gasar Premier.

Mataimakin shugaban kulob din Craig Shakespeare ya maye gulbinsa, inda ya ya nasara a wassani biyar da kuma nasara da ya yi a gasar Champions League da suka kara da kulob din Sevilla.

Bayan an sallami Mista Ranieri, rahotanni na nuna cewa wasu 'yan wasan kulob din sun taimaka wajen korarsa, kamar Jamie Vardy da Kasper Schmeichel, inda suka musanta zargin.

Mista Raneiri ya kara da cea, "Na ji maganganu da dama," ama kocin dan shekera 65 bai fadi ko wa yake zargi da shirya masa gadar zaren ba.

"Ba na so na fadi ko waye. Ni mutum ne mara munafunci. Duk abin da zan fada, na fade shi a gaban mutumin," in ji kocin.