Cristiano Ronaldo ya zura kwallaye 100 a gasar Turai

Cristiano Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Cristiano Ronaldo ya zura kwallaye 100 a Gasar Zakarun Turai

Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo shi ne ya fi kowa zura kwallaye a gasar Turai inda a yanzu yake da kwallaye 100 sakamakon biyun da ya zura a ragar Bayern Munich a ranar Talata.

Ronaldo ya zura kwallo biyu a zagaye na biyu na wasan da Madrid ta doke Bayern da ci 2-1 a gasar cin kofin zakarun Turai.

Arturo Vidal ne ya fara ciyo wa Bayern kwallo, amma daga bisa kuma ya barar musu da fenaritin da ya hana shi cin kwallo ta biyu.

Daga nan ne sai Ronaldo ya ciyo wa Madrid kwallo ta farko.

Har ila yau, an bai wa dan wasan Bayern Javi Martinez jan kati abin da ya dawo da 'yan wasansu zuwa 10. Sai dai mai tsaron gidansu Manuel Neuer ya jajirce, inda ya kare munanan hare-hare daga Gareth Bale da Karim Benzema da kuma Ronaldo.

Sai dai ana cikin haka ne, Ronaldo ya mamayi golan ya jefa masa kwallo a raga, wadda ta wuce ta tsakanin kafafunsa.

Duk da nasarar da ta samu, Real Madrid tana iya yin takaici game da yadda suka so shige wa gaban Bayern sosai gabanin karawar da za su kara yi a gidansu wato filin wasa na Bernabeu a mako mai zuwa.