An kai wa Borussia Dortmund hari

An dage wasan Borussia Dortmund da Monaco

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An sanar da dage wasan zuwa Laraba, 12 ga watan Afrilun 2017, da misalin 6:45 na yamma

An dakatar da wasan da Borussia Dortmund ke shirin bugawa da Monaco da karfe 7:45 na yammar ranar Talata, zuwa Laraba da misalin 6:45 da yamma.

Rahotanni sun ce wani abu ya fashe a filin wasanni a Jamus, kusa da bas din tawagar Borussia Dortmund, da ke wajen otal din da suka sauka.

Tawagar ta tabbatar wa manema labarai cewa, mai tsaron gidan Marc Bartra ya samu rauni sakamakon harin, amma kuma sun ce babu sauran wata barazana ga filin wasannin.

Masoya kwallon kafa sun taru cikin filin wasannin, inda suke jira su ji ko za a buga wasan daren Talatan, a yayin da babban talabijin din da ke kafe a filin ke nuna bayanai kan lamarin.

Borussia Dortmund sun tabbatar da cewa suna kan tattaunawa da hukumar kula da kwallon kafa ta Turai, watau UEFA, da kuma jami'an tsaro, kan lamarin.