Bani da hannu a korar Ranieri — Shakespeare

Craig Shakespeare

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Ba mu taba samun sabani ko rashin jituwa da Raneiri ba

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Leicester City, Craig Shakespeare ya ce, "bai taba samun sabani" da tsohon kocin kungiyar Claudio Ranieri ba.

Lecister City ta kori Ranieri ne a watan Fabrairu, kuma a ranar Litinin ne ya ce, "Wani ne ya shirya masa tuggu" da ya jawo aka kore shi.

Da yake mayar da martani kan zargin da Raneiri din ya yi, Shakespeare ya ce, " Bamu taba samun sabani ko rashin jituwa da shi ba.

Ya ce, "Kowa yana da 'yancin magana. Bani da wata matsala da wannan. Zuciyata daya game da wannan".

Ranieri dai ya fada wa kafar yada labarai ta Sky Sports a ranar Litinin cewa, wani ne a kungiyar ya shirya masa gadar-zare, amma kuma bai kama suna ba, sai dai hakan ya janyo wa Shakespeare tambayoyi masu dimbin yawa daga manema labarai game da lamarin.

Shakespeare, ya ce ya yi magana da Ranieri, a ranar da aka kore shi, kuma ya yi amanna cewa suna da kyakkyawar alaka.

Ya kara da cewa, "Don haka ina nan a kan matsayata da na fada a tattaunawata ta farko, a matsayin sabon Koci cewa, na yi magana da Ranieri a daren da aka kore shi, ya gode min, kuma ni ma na gode masa."

Leicester City, dai na kasar Spaniya a karawar da za su yi da Atletico Madrid, a zagayen farko na wasan dab da kusa da na karshe na Zakarun Turai a ranar Laraba da daddare.