An tsare wanda ake zargi da kai harin Borussia Dortmund

ana bincike game da wasiku guda biyu da suka dauki alhakin harin.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana bincike game da wasiku guda biyu da suka dauki alhakin harin.

'Yan sanda a kasar Jamus sun tsare wani mai kaifin kishin Islama wanda ake zargi da kai hari kan motar 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund.

Masu gabatar da kara sun ce daya daga cikin abubuwa ukun da suka fashe ranar Talata na dauke da siraran karafa.

Sun ce ana bincike game da wasiku guda biyun da suka dauki alhakin harin.

Mai magana da yawun babban mai gabatar da kara na kasar Frauke Koehler, ta fada a Karlsruhe, cewa, "Binciken namu zai mayar da hankali ne kan mutum biyu da ke da alaka da kaifin kishin Islama. Ana gudanar da bincike kan gidajensu. Kuma an tsare daya daga cikinsu.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta fada ranar Laraba cewa harin babban laifi ne, kuma ta yaba wa magoya bayan kungiyar saboda hadin kai da suka nuna.

Harin dai wanda aka kai a ranar Talata da daddare, ya sa an dage wasan da kungiyar ke shirin fafatawa da kungiyar Monaco a gasar Zakarun Turai, zuwa ranar Laraba da misalin karfe 6:45 agogon Najeriya.