Magoya bayan Leicester sun yi gumurzu da 'yan sandan Madrid

Injured Leicester City Fan
Bayanan hoto,

Wakilin BBC Phil Mackie, ya ga magoya bayan da suka ji ciwo a Plaza Mayor

An yi rikici tsakanin magoya bayan Leicester City da 'yan sandan Spaniya kafin karawarsu da Atletico Madrid a gasar Zakarun Turai.

Hotunan bidiyo na kafafan sada zumuntar zamani wadanda aka nada a Plaza Major, sun nuna magoya bayan kulob din wadanda suka ji ciwo da kuma jami'an tsaro sanye da rigunan sulke inda suke rike da sanduna.

Wakilin BBC, Phil Mackie, ya tabbatar da cewar 'yan sanda sun yi amfani da sanduna domin korar mutane daga sassan dandalin.

Da farko, 'yan sandan Spaniya sun ce, an kama magoya bayan Leicester takwas domin sun jawo hargitsi a daren Talata.

Bayanan bidiyo,

Magoya bayan Leicester City sun yi fada da 'yan sandan Spaniya a Madrid

Bidiyon da aka wallafa a Intanet ya nuna ana jifan wasu jami'ai yayin da magoya baya ke ihun "Gibraltar tamu ce" a dandalin Plaza Major, inda aka bai wa magoya bayan Leicester damar haduwa.

Wani ganau ya shaida wa BBC 5 cewar: "Akwai wasu mutane wadanda kila sun bata wa 'yan sanda rai, amma sai suka huce a kan dukkan mutanen da ke wajen.

"Akwai wasu mutane dauke da yara, sun shigo da sanduna kuma akwai wani mutum mai shekara 70 da kuma yara a daidai hanyar da abin ya faru."

Asalin hoton, marklcfc1976

Bayanan hoto,

Magoya bayan Leicester wadanda ran su ya baci sun wallafa hotunan abokansu da suka ji ciwo a kafafen sada zumunta na zamani

Wakilin BBC Owynn Palmer-Atkin, ya ce "Wuta ta tashi sama sau biyu da shudin hayaki, sai kuma wata kara ta biyo baya. A lokacin ne kuma salon ihun sa ake ya sauya."

Ya kara da cewar: "Da alamar hayaniyar taron mutanen ta yi kasa, sannan sai abin ya zama fargaba.

"An sake yin wata kara, lokacin ne motocin kwantar da tarzoma suka fara dannawa cikin dandalin. Na yi mamakin cewar motar 'yan sanda za ta iya tafiya da irin wannan saurin a dandalin da ke cike da mutane."

Wani mai gabatarwa na BBC ,Gary Lineker, kuma mai goyon bayan Leicester City ya wallafa a shafinsa na Twitter cewar: "Na ga bidiyon wasu magoya bayan Leicester suna rashin da'a a Madrid. 'Yan tsiraru bata gari sun bata lamarin. Wannan abin bacin rai ne."

Bayanan bidiyo,

Wani mai goyon bayan da 'yan sanda 'suka daka' ya nadi bidiyon rikicin

A daren Talata Phil Mackie ya ce ya shaida abin da ya yi kama da wani harin na ba-gaira-ba-dalili kan magoya baya.

Ya bayar da rahoton cewar ya ga 'yan sanda sun yi kan wasu magoya bayan Leicester kafin su tura uku daga cikinsu har kasa. Kana suka dake su da kulki sannan suka wurga su bayan mota a-kori-kura.

'Yan sanda sun ce an far wa jami'ansu shida a rikicin.

Har yanzu magoya bayan kungiyar takwas da aka kama suna tsare kuma za su gurfana a gaban kotu ranar Alhamis.

Bayanan bidiyo,

'Yan sandan kwantar da tarzoma sun ja daga da magoya bayan Leicester a dandalin Madrid square