Fenaretin Atletico Madrid na boge ne — Shakespeare

Bayanan bidiyo,

An cuci Leicester - Shakespeare

Kociyan Leicester, Craig Shakespeare, ya ce lafiri canki-canki ya yi game da hukuncin fenaretin da ya bai wa Atletico Madrid, a wasan da ya kulob dinsa ya sha kaye a hannun Madrid din a wasan karo na farko a matakin kusa da dab da na karshe a gasar Zakarun Turai.

Lafiri Jonas Eriksson, ya bayar da fenareti kan ketar da aka yi kan Antoine Griezmann kuma hotunan bidiyo na nuni da cewar laifin ya auku ne a wajen yadi na 18 na Leicester.

Griezmann ya sha fenaretin, abin da ya bai wa Atletico nasara a Spaniya.

"Hukuncin da lafirin ya yi mai ban haushi ne," in ji Shakespeare.

"Wani muhimmin lokaci ne a wasan. Dole ya yi dai-dai a wannan lokacin, bai kamata ya yi canki-canki game da wadannan abubuwan ba. Lalli bugun tazara ne, amma a wajen yadi 18 ne.

"Wani muhimmin hukunci ne da za ka so a gyara."

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Marc Albrighton ya fara taba dan Atletico ne daga wajen yadi 18

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

... amman faduwar Griezmann ta kai shi cikin yadi 18

Shi ma mai tsaron gidan Leicester City, Kasper Schmeichel, shi ma ya hakikance cewar hukuncin bai yi dai-dai ba.

"Wani hukunci ne mai wuyar dauka. Ya kamata mu samu wani abu daga wannan (wasan), amman mun yarda da sakamakon.

Asalin hoton, Reuters