An sayar wa 'yan China AC Milan

Berlusconi

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

AC Milan ta lashe gasa 29 a karkashin Berlusconi

Kamfanin Rossoneri Sport Investment Lux na China ya sayi kungiyar kwallon kafa ta AC Milan kan kudi fam miliyan 628m.

Kamfanin ya sayi kungiyar daga hannun tsohon Firayim Ministan Italiya, Silvio Berlusconi, wanda ya mallake ta tun shekarar 1986 da alkawarin kara jarin kungiyar.

A lokacin da kuniyar take hannun Berlusconi, ta lashe kofin gasar kungiyoyin kwallon kafa na Italiya takwas da kuma kofin Turai biyar.

Amma Milan ba ta lashe gasar Seria A ba tun shekarar 2011 kuma ta zo ta 10 da kuma ta takwas a gasar a shekarun da suka wuce.

A yanzu kungiyar na matsayi na shida, yayin da suke bayan kungiyar da ke kan gaba a gasar da maki 20.