Mata ba zai buga sauran wasannin Man Utd ba

Juan Mata Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mata ya koma United a kan £37 lokacin shugabancin David Moyes

Dan wasan tsakiya na Manchester United Juan Mata ba zai buga wasannin da suka ragewa kungiyar ba saboda tiyatar da aka yi masa a cinyarsa.

An yi wa dan wasan dan kasar Spain tiyata a watan jiya sai dai ya yi tsammanin zai buga wasannin da suka ragewa kungiyar a kakar wasa ta bana.

Sai dai kocin United Jose Mourinho dan wasan mai shekara 28, wanda kungiyar ta saya da Chelsea a watan Janairun 2014, ba zai buga wasa ba sai karshen watan Mayu.

Mourinho ya kara da cewa Phil Jones da Chris Smalling ba za su dawo ba sai tsakiyar watan Mayu.

Za a kawo karshen kakar wasan Premier ne a ranar 21 ga watan Mayu.

Labarai masu alaka