Tottenham na bai wa Chelsea tsoro - Frank Lampard

Frank Lampard

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Lampard ya ci gasar Premier uku da Chelsea

Wasannin da Tottenham ke buga wa masu cike da ban sha'awa da hazaka za su yi matukar gigita Chelsea, wacce ke kan gaba a saman teburin gasar Premier, a cewar tsohon fitaccen dan wasan na Stamford Bridge Frank Lampard.

Tottenham ta Bournemouth sau bakwai a jere inda tazarar maki hudu ne kawai tsakaninta da Chelsea kafin wasan da za su yi da Manchester United ranar Lahadi.

Lampard ya shaida wa BBC Sport cewa, "Chelsea na sane sarai da tasirin da Tottenham ke da shi. Hakan na ba ta tsoro amma dai haka za ta hakura."

Da yake jawabi bayan wasan da Tottenham ta doke Bournemouth 4-0, okcin Spurs Mauricio Pochettino ya ce kungiyar tasa ta samu ci gaba tun wata 12 da suka gabata kuma a shirye take ta zakuda gaba domin lashe kofin Premier.

Ya kara da cewa, "Mun kwashe tsawon lokaci muna fafatawa da Leiceste da Chelsea da kuma 'yan jarida. Mun yi fada da kowa. Amma yanzu mun mayar da hankali wurin daukar kofin."

Chelsea za ta dawo da kimarta da maki bakwai da kuma ragowar wasa shida idan suka doke Manchester United da kuma tsohon shugabansu Jose Mourinho a Old Trafford.