Kun san unguwar da ta 'haifi' manyan 'yan ƙwallon Nigeria?

Taribo West

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Taribo West na daya daga cikin manyan 'yan kwallon da aka haifa a Ajegunle

Unguwar Ajegunle ta fi suna a matsayin wurin da ke da hatsari a birnin Lagos da ke kudu maso yammacin Najeriya, amma ta yi suna a wurin wani abin - samar da wasu daga cikin fitattun 'yan kwallon kafar da suka fito da sunan kasar a duniya. Kun san abin da ya sa unguwar ta samu wannan nasara?

Najeriya da tana da mutanen da ke da matukar sha'awar kwallon kafa, don haka ba abin mamaki ba ne idan kowanne bangare na kasar ya samar da fitattun 'yan wasa, amma lamarin Ajegunle, ko AJ City, kamar yadda ake kiran unguwar, daban yake.

Tun farkon shekarun 1990 ake samun shahararrun 'yan kwallon kafa daga Ajegunle. Wasu daga cikinsu su ne Taribo West, Odion Ighalo, Brown Ideye, Samson Siasia, Obafemi Martins, Taribo West da kuma Jonathan Akpoborie.

Rayuwa na da matukar wahala ga mazauna Ajegunle.

Suna fama da matsalar rashin tsaro da rashin ruwan sha da na wutar lantarki da kiwon lafiya.

Amma mene ne ya sa Ajegunley ta yi fice wajen samar da 'yan kwallon kafa? Za a iya cewa ta yi fice ne saboda unguwa da ta hada kowa da kowa.

"Al'uma ce da ta hada mutane da suka fito daga kabilu daban-daban," in ji Bennedict Ehenemba, wani mai horas da 'yan kwallon kafa a kasar Jamus, wanda ya tashi a Ajegunle.

Ya kara da cewa, "Akwai Yarabawa da kabilar Igbo da Hausawa da Itsekiri da sauran kabilun Najeriya zaune a Ajegunle. Ka ga kuwa wannan hatsin-barar na nuna cewa akwai hikimi da basira a wannan unguwa."

Bayanan hoto,

Matasa na da filin kwallo a Ajegunle

Yawancin matasan da suka yi fice a fagen kwallon kafa a wannan unguwa sun soma murza leda ne a filayen wasan makarantar St Mary's Catholic Church da na barikin sojoji na sojin ruwa.

Su ne wuraren da matasa za su yi wasa ba tare da fuskantar matsala ba.

Sauran filayen wasan da na matsala inda 'yan iskan unguwa wadanda aka fi sani "Area Boys" ke bukatar a ba su kudi kafin su bar matasan su buga wasa.

Fitaccen dan wasan Super Eagles Jonathan Akpoborie, wanda ya yi suna a gasar Bundesliga ta Jamus a shekarun 1990, ya soma wasansa a wadannan filayen wasa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jonathan Akpoborie ya buga wasa a Jamus a shekarun 1990

Unguwar tana da wani tsari da ke karfafawa matasan 'yan wasa gwiwa.

Hakan ne ya sa suke yi zarra fiye da 'yan wasan da ke murza leda a makarantun koyar da kwallon kafa.

Alfred Emuejeraye, wanda ya yi suna a wasannin lig-lig na Switzerland, ya girma a Ajegunle.

Ya yi amannar cewa Ajegunle ta yi fice a duniya ne saboda nasarar da ta samu a fannin kwallon kafa.

"Mutanen wannan unguwa na kaunar kwallon kafa, komai ka gani a nan yana da alaka da son tamaula don haka mu anan muna auna nasara ne da fice a fagen kwalon kafa," in ji shi.

Odion Ighalo - tsohon dan wasan Watford FC wanda yanzu yake buga wasa a kungiyar Changchun Yatai FC ta China - dan asalin Ajegunle ne.

Yanzu yana zaune a wasu daga cikin manyan biranen duniya, amma bai manta da Ajegunle ba.

A cewarsa, "Abu ne mai wahala yin rayuwa a can. Ba wuri ne da za ka samu duk abin da kake so ba, kamar Turai. Dole ka zage damtse domin samun kudin da za ka sayi rigar kwallo da takalma da kudin zuwa filin wasa da ma ruwan da za ka sha bayan ka yi atisaye."

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Odion Ighalo - wanda ke buga wasa a kungiyar kwallon kafar Changchun Yatai FC ta China - ya girma a Ajegunle

Wasu daga cikin fitattun 'yan wasan da suka girma a Ajegunle na komawa can domin horas da matasan da ke sha'awar kwallon kafa da zummar rike wannan kambu na kasancewa unguwar da ta shahara wajen samar da fitattun 'yan wasan kwallon kafa.