Liverpool ta doke West Brom da ci 1-0

Liverpool

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Roberto Firmino ya zura kwallaye 11 kenan a kakar Premier ta bana

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta yi nasarar komawa mataki na uku a teburin gasar Premier ta Ingila, bayan da ta lallasa West Brom da ci 1-0.

Roberto Firmino ne ya zura kwallon da kai kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Yanzu Liverpool ta na da maki 66, inda take bin bayan Tottenham wacce ke mataki na biyu da maki 71.

Liverpool ta yi nasarar lashe wasanni biyar kenan a wasanni bakwai, inda ita kuma kungiyar West Brom ta sha kashi sau uku a jere.