Antonio Conte ya dauki alhakin kayen da Chelsea ta sha a wajen Man U

Bayanan bidiyo,

'Yan Man Utd sun fi nuna shauki da kishi- Conte

Kociyan Chelsea, Antonio Conte, ya ce ya dauki alhakin kasa zaburar da 'yan wasan kungiyarsa a kayen da ta sha a hannun Manchester United a ranar Lahadi.

Chelsea ta sha kaye a filin wasan Old Trafford, abin da ya sa ratar da ta ba wa Tottenham da ke binta a kan teburin Firimiya ya zama maki hudu, sabanin ratar maki goman da ta jagoranci teburin da shi tun a watan Maris.

"Ba mu yi wasa mai kyau ba, kuma United ta cancanci lashe wasan," In ji Conte.

"Sun fi nuna shauki da kishi da kuma muradi. A wannan yanayi laifin na kociya ne."

Dan asalin Italiyan ya kara da cewar shi ya kasa "mayar da hankalin da ya dace domin lashe wasan".

Kungiyar Spurs ta shiga takarar cin kofin Firimiyar bayan ta lashe wasanni bakwai a jere a lokacijn da Chelsea ta sha kaye sau biyu a wasanni hudun da ta yi a baya-bayan nan.

Kungiyoyin biyu za su hadu a a filin wasan Wembley a ranar Asabar, a wasa na farko a jerin wasannin kusa da na karshe na cin kofin Ingila wadanda za a buga a karshen mako.

"Na damu domin dole mu yi aiki tare kuma mu samu kishin da ya dace domin lashe kofin," In ji Conte.

"Idan wani yana tunanin ba wani abin a-zo-a-gani ba ne cewe Chelsea ta lashe gasar, mun fara gasar bana a matsayin wadanda ba a ganin za su tabuka wani abu ba, bayan mun tsaya a lamba ta goma a gasar bara.

"Tottenham tana wasa da kyau, kuma tana wasa da karsashi. Dole muma mu samu irin wannan yanayin."

Courtois ya ji ciwo a wasan kwando?

Shirin Chelsea na karawa da kungiyar Jose Mourinho ya samu cikas a lokacin da mai tsaron gida, Thibaut Courtois, ya ji rauni a idon kafarsa a makon da ya gabata.

The Blues ta kuma rasa dan wasan baya, Marcos Alonso, 'yan wasu mintoci kafin a fara wasa saboda rashin lafiya.

An tambayi Conte kan rahotannin da ke cewa dan asalin kasar Belgium, Courtois, ya ji ciwo a lokacin da ya ke buga wasan kwallon kwando a wani wasan sada zumunta.

Sai dan Italiya ya ce: "Bayan shan kaye bai kamata mutum ya koma cikin irin wannan yanayin ba.

"Courtois ya ji ciwo a tsakiyar mako kuma saboda haka bai samu buga wasa ba. Amma ina ganin ya fi kyau mu mayar da hankali kan wasan, kar mu rinka neman uzuri."

Bayanan bidiyo,

MOTD3: An fara rige-rigen lashe gasar?

Bayanan bidiyo,

Mourinho ya ce Man Utd 'ta hana Chelsea sakat'