John Terry zai bar Chelsea

John Terry

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Terry ya buga wa Chelsea wasanni 713 tun da ya fara taka mata leda a shekara 1998

Jagorar teburin gasar Firimiya, Chelsea, ta ba da sanarwar cewar Keftin dinta, John Terry, zai bar kungiyar a karshen kakar bana.

Terry, mai shekara 36 da yake buga baya ta tsakiya, ya buga wa Chelsea wasanni 713 tun da ya fara taka mata leda a shekarar 1998, kuma sha mata kwallaye 66.

Ya kansace keftin din Chelsea a wasanni 578 - adadin da babu wanda ya taba yi - amma a kakar bana ya fara wa kungiyar wasanni hudu ne kawai a gasar Firimiya.

Terry ya ce:"Ina jin ina da gudumawa mai yawa da zan iya bayarwa a kan fili, amman na fahimta cewar damar da zan iya samu a Cheslea ba ta da yawa."