An sanar da sunan Harry Redknapp a matsayin sabon kociya Birmingham City

Harry Redknapp

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Harry Redknapp ya fara aiki a matsayin kociya ne a Bournemouth a shekarar 1983

Birmingham City ta ba nada Harry Redknapp a matsayin kociyan ta.

Rednapp wanda tsohon kociyan West Ham da Tottenham da kuma QPR ne zai gaji Gianfranco Zola, wanda ya bar aiki ranar Litinin bayan takwarar kungiyarsa da ke kasa-kasa a teburin gasar Championship, Burton Albion, ta doke Birmingham City.

'Yan Birmingham din su ne na 20 a teburi da maki uku saman jerin masu faduwa zuwa mataki na kasa, kuma za su ziyarci abokan gogayyarsu, Aston Villa ranar Lahadi.

Redknapp mai shekara 70 ya shaida wa Talksport cewar: "Birmingham wata kungiyar kwallon kafa ce mai nagarta, amman ta na cikin wani hali na rashin tabbas."

An sanar da nadin Redknapp ne sa'o'i 16 bayan Zola ya bar aiki, kuma Redknapp zai yi aiki ne zuwa karshen kakar bana a matakin farko.

Ya kama aiki a matsayin jagoran Jordan a wasannin zuwa gasar cin kofin duniya guda biyu a bara, kuma ya yi aiki a matsayin mai ba da shawara ga kulub din Derby County a kakar bara, amma bai yi aikin kociya a Ingila ba tun shekarar 2015.

Kociyan ya lashe kofin kalubale da Portsmouth a shekrar 2008, ya kuma kai Tottenham matakin kusa da dab da na karshe a gasar zakarun Turai.

A shekarar 2016, an nada shi darakata a Wimborne Town da kuma kwararre mai ba da shawara ga kungiyar kwallon kafa ta Central Coast Mariners.

'Ba zan mayar da su Real Madrid ba'

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Steve Cotterill (a hagu ) ya yi aiki da Harry Redknapp atQPR

Redknapp, wanda tsohon kociyan Bristol City, Steve Cotterill, zai yi aiki da shi a matsayin mataimaki, ya ce: "Mutanen Birmingham sun kira ni karfe bakwai na daren jiya.

"Na je Londan da mota inda nagana da su tsawon kusan minti 15, kuma na gaya mu su:'Zan zo in yi.'

Labarin ya bawa matata mamaki 'kana hauka ne?' in ji ta. Amma na gaji da zama ba na komai."

Birminghma ka iya shiga cikin jerin masu faduwa daga gasar Championship a lokacin da Redknapp zai karbi ragamar kungiyar.

Idan Blackburn da Nottingham Forest suka lashe wasanninsu ranar Lahadi, Birmingham za ta fada cikin kulob uku na kasan teburi.

Bayan ta hadu da Villa, Birmingham za ta karbi bakuncin Huddersfield Town da ke neman shiga gasar Firimiya kafin su kai ziyara Bristol City a karshen kakar bana.

"Babban kalu bale ne," in ji Redknapp. "Zan zauna a kungiyar zuwa karshen kakar bana, amman in na iya tabbatar da su a gasar, zan zauna domin mu tattauna yadda za mu tunkari kakar badi.

"Hakika babu hatsari a lamarin. Sun lashe wasanni biyu cikin 22. Bani da sandar sihiri. Ba zan mayar da su Real Madrid ba. Muna bukatar wata nasara."