An kama tsohuwar matar shugaban Boko Haram

.

Asalin hoton, .

Bayanan hoto,

Jami'an Civil Defence tare da 'yan matan a cikin hijabi. Boko Haram tana amfani da matan wajen kai hare-haren kunar bakin wake

Jami'an tsaron rundunar tsaro ta farin kaya a Najeriya sun kama wata tsohuwar matar shugaban wani bangare na Boko Haram, Mamman Nur, a birnin Maiduguri.

Kwamanadan rundunar jami'an tsaron na jihar Borno, Ibrahim Abdu, ya gabatar da Fatima Kabir yar shekara 15 wadda ya ce ta amsa cewar ita tsohuwar matar Mamman Nur ce.

Rundunar tsaron ta ce jami'anta sun kama Fatima ne tare da wata mai suna Amina Salisu a lokacin da suke watangaririya a tashar mota da ake kira Kano Park a birnin Maiduguri ba tare da alamar akwai inda za su ba.

Ko da jami'an tsaron suka musu tambayoyi sai suka amsa cewar an shigo da su Maiduguri ne da nufin kai hare-haren kunar bakin wake.

Kwamandan rundunar tsaro ta farin kayan ya ce bayan anyi wa Fatima gwaji an gane cewar tana dauke da cikin wata hudu.

Har ila yau Ibrahim Abdu ya ce da zaran rundunar ta gama bincike za ta mika matan ga hukumomin domin yin abin da ya dace.