Kisan dan wasan Panama: An kama mutum 4

Panama

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An kashe dan wasan ne a gaban gidansa a birnin Nuevo Colón

'Yan sandan kasar Panama sun ce suna tsare da mutum hudu bisa zarginsu da hannu a kisan wani dan wasan kwallon kafan kasar Amílcar Henríquez.

Duka mutanen da aka kama ba su wuce shekara goma sha ba, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

An harbe dan wasan mai shekara 33 ne har lahira yayin da yake barin gidansa da ke birnin Nuevo Colón a ranar Asabar. Hakazalika, an kashe wani mutum mai shekara 36 mai suna, Delano Wilson.

Kafafen yada labaran kasar sun ce Mista Wilson abokin marigayin ne. Sai dai 'yar uwan Wilson ta ce ya mutu ne a kan hanyarsa ta zuwa sayo abinci.

Har yanzu ba a san dalilin kisan ba, amma 'yan sanda sun ce ga alama an kitsa harin ne.

'Yan sandan sun ce maharan sun jira isowar Mista Henríquez ne a wani gida da yake kallon na marigayin.

An hana wata dattijuwa mai shekara 70 da wasu 'yan mata uku da suke zaune a gidan, fita daga kasar don ci gaba da bincike.

Mista Henríquez yana buga wa tawagar kasar Panama da kuma wani kulob din kasar Árabe Unido.

Shugaban Kasar Panama Juan Carlos Varela ya yi Allah-wadi da kisan a shafin na Twitter, kuma ya ba da tabbacin cewa za a yi adalci kan al'amarin.