Ɗan sanda mai lalata a bakin aiki ya gamu da gamonsa

Devon and Cornwall
Bayanan hoto,

Sai da aka gudanar da zaman sauraro na sirri kafin a kori wannan ɗan sanda mai lalata da mata

An sallami wani ɗan sanda daga aiki saboda yin lalata da mata sau da dama a bakin aikinsa tsawon shekara biyu cikin yankin Devon da Cornwall a Ingila.

Ɗan sanda wanda ba a bayyana sunansa ba, ya aikata baɗala da mata biyu waɗanda ya gamu da su lokacin da yake bakin aiki da ofishin 'yan sandan shiyyar Devon da na Cornwall.

An gudanar da zaman sauraron wannan bahasi cikin sirri a shalkwatar 'yan sanda ta Exeter makon jiya.

Zaman sauraron ya ji yadda ɗan sandan a wani lokaci ya haike wa wata mata da ke cikin halin ni-'ya-su a bakin aikinsa.

Ya kuma taɓa fitar da bayanan sirrin hukuma, don haka aka sallame a kan aikata ba daidai da kuma cin amana.

Ayarin jami'an zaman sauraron ya samu ɗan sandan "da keta ƙa'idojin aikin ɗan sanda, " musammam waɗanda suka jiɓanci tsare sirri, haƙƙoƙi da nauye-nauye, oda da umarni, tsare gaskiya da ƙimar aiki.

Wata sanarwa ta ce: "Jami'in ya gaza kiyaye nauye-nauyen da ke kansa a shekara ta 2012 zuwa 2014, a lokuta da dama ta hanyar aikata lalata a bakin aiki, ciki har da saduwa da wata shaida da ke cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi."

An sallami wani ɗan sandan ma wata biyar da ya wuce saboda yin lalata da wata mata.