Barcelona: Dole ne mu taka rawar gani a wasanmu da Juventus

"Dole ne mu taka rawar gani.. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dole ne mu zage dantse.

Kocin Barcelona Luis Enrique ya ce za su "fuskanci wani dare na musamman" yayin da kungiyar ke shirin kabar bakuncin Juventus a zagaye na biyu na wasan dab da kusa da na karshe na kofin zakarun Turai a daren Laraba.

Barcelona wacce ta doke Paris St-Germain 6-1 bayan da PSG ta doke ta 4-0 a wasan farko a zagayen da ya gabata, na bukatar maimaita irirn wannan bajinta ga Juventus a daren na Laraba, bayan da Juventus din ta doke ta 3-0 a makon da ya gabata a Italiya.

Ya ce "Dole ne mu tashi tseye mu nuna kwazonmu domin mu kai ga gaci.

Fatanmu shi ne kada mu yi kuskure a duka harin da muka kai, domin kuwa burinmu shi ne, mu ci kwallo biyar"

Barcelona dai ta kafa tarihi a gasar ta zakarun Turai, bayan da a watan da ya gabata ta zama ta farko da ta rama ci 4-0 da aka yi mata a zagayen farko, sannan a zagaye na biyu ta ci 6-1, abinda ya sa ta samu damar zuwa wasan dab da na kusa da na karshe karo 10 a jere.

Enrique ya ce "wadanda suka kalli wasanmu da PSG, yanzu ma suna da damar sake kasancewa da wani dare mai matukar tarihi"

Labarai masu alaka