Me Trump ya yi wa lakcaran da ya ce a rataye shi?

Fresno University Lecturer Hakkin mallakar hoto FRESNO STATE UNIVERSITY
Image caption Saƙon Twitter na malamin ya ja hankalin hukumomin leƙen asirin Amurka da ke gudanar da bincike a kan batun

An dakatar da wani malamin jami'a a Amurka bayan ya wallafa saƙo a shafinsa na Twitter da ke cewa kamata ya yi a rataye shugaba Donald Trump.

Jami'ar Fresno da ke tsakiyar California ta faɗa a cikin wata sanarwa cewa Lars Maischak ya "amince da dakatar da aiki bisa raɗin kansa".

A ranar 18 ga watan Fabrairu ne malamin ya buga cewa: "In dai ana son ceto dimokraɗiyyar Amurka, to sai an rataye Trump. Da zafi-zafi kan bugi ƙarfe."

Hukumar tsaron farin kaya ta FBI da saura jami'an leƙen asiri na gudanar da bincike a kan saƙon.

Sanarwar ta ce: "Yayin zaman dakatarwar tasa, Dr Maischak ba zai ci gaba da koyarwa ba, sai dai zai ci gaba da gudanar da ayyukan bincike a wajen harabar jami'ar."

Tun farkon wannan wata ne, malamin ya rubuta a cikin wata sanarwa da ya aika wa wata kafar yaɗa labarai cewa ya ji "takaicin yadda shugaban jami'ar ya sanya kansa cikin gangamin ɓata-suna".

Malamin - wanda ke koyar da tarihin Amurka a jami'ar Fresno tun shekara ta 2006 - ya ce ba gaskiya ba ne zargin da ake yi masa cewa yana da mugun nufi ga shugaba Trump".

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaban Amurka Donald Trump

Ya kuma kare wani saƙon Twitter da ke cewa: "#TheResistance wato a bijire da kuma #ethniccleansing Justice, wanda ke kira a zartar da hukuncin kisa kan 'yan jam'iyyar Republican biyu a kan duk wani baƙon haure da aka kora daga Amurka."

Saƙon Mr Maischak a kan shugaba Donald Trump - ga mutum 28 da ke bin shafinsa - bai wani ja hankali sai bayan da wata kafar yaɗa labarai ta intanet ta yayata shi.

Kafar labaran Breitbart ta ce kalaman malamin jami'ar "na bayyana dalilan da suka sa Amurkawa ke yi wa jami'o'i kallon raini a faɗin ƙasar".

Dr. Maischak ba shi ne mai sukar lamirin shugaban Amurka na farko da ke ganin iyakar 'yancin albarkacin faɗar baki ba.

Shi ma mawaƙi Snoop Dogg ya harba bindigar wasa ga wani da ya shigar Donald Trump a wani bidiyon waƙarsa na baya-bayan nan.

Donald Trump a saƙon Twitter ya mayar da martani da cewa: "Ko kun san yaya mutane za su ji idan @SnoopDogg, da ke fuskantar koma-bayan harkoki, ya nuna bindiga kuma ya harbi Shugaba Obama? Sai Ɗauri a gidan yari!"

Yayin wani maci na mata a Washington cikin watan Janairu, fitacciyar mawaƙiya Madonna ta ce ta riƙa "tunanin kawai ta je ta tarwatsa fadar White House".

Labarai masu alaka