Ta faru ta ƙare wa Barcelona

Juventus team Hakkin mallakar hoto @juventusfcen
Image caption 'Yan wasan Juventus na murnar samun nasarar zuwa zagayen kusa da ƙarshe a gasar cin kofin Zakarun Turai

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus ta yi amfani da wani irin salon tsare gida na musammam don kai wa ga zagayen kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin Zakarun Turai.

Juve ta dage a filin wasa na Nou Camp ta hana Barcelona jefa mata ƙwallo.

Bayan ci 3 -0 a karawarsu ta farko, Barcelona ta yi ta lailaya ƙwallo a wasansu na biyu, sai dai ta gaza maimata abin da ta yi wa Paris St-Germain, wadda ta jefa mata ƙwallo 4 -0 tun da farko.

Lionel Messi wanda tun farko golan Juventus Gianluigi Buffon ya hana shi dama, ya sharara wani ƙwallo da ya tsallake raga ya wuce.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Giorgio Chiellini (dama) ya yi amfani da ƙwarewarsa wajen taimaka wa ƙungiyarsa tsare gida don zuwa zagayen kusa da na ƙarshe

Luis Suarez da Neymar su ma sun ɓaras da damammaki a daren Larabar da ƙwaƙƙwaran harin da Barcelona ta kai ya tsaya a ɗaya kacal.

Gonzalo Higuan na Juventus ya maka ƙwallon da golan Barce ya kama, yayin da Juan Cuadrado shi ma ya ɓaras da dama.

An tashi wasa babu ci, lamarin da ya bai wa Juventus nasara da ci 3 -0.

ƙungiyar ta Italiya a yanzu ta bi sahun Real Madrid da Atletico Madrid da Monaco don karawa a wasan kusa da ƙarshe.

Labarai masu alaka