'Jami'an gwamnati sun karkatar da biliyoyin kuɗi'

Nigeria Senate Floor Hakkin mallakar hoto FACEBOOK
Image caption Kwamitin Shehu Sani ya ce a shirye yake ya taimaka wa binciken da gwamnatin Nijeriya ke yi dakataccen sakataren

Shugaban kwamitin majalisar dattijai da ya binciki zargin karkatar da tallafin 'yan gudun hijira, ya ce matakin dakatar da sakataren gwamnatin tarayya ya nuna cewa Buhari ya ɗauki hanyar ba-sani-ba-sabo.

Sanata Shehu Sani ya ce jami'an gwamnati sun karkatar da biliyoyin kuɗin da aka ware don taimaka wa 'yan gudun hijira.

"Mun gano cewa biliyoyin kuɗaɗe da ya kamata a yi amfani da su wajen taimaka wa marayu, 'yan gudun hijira da yawa an kau da su. Jami'an gwamnati sun sa a cikin nasu jakunkuna."

A cewarsa kafin wannan lokaci zargin da ake yi shi ne idan kana jam'iyya mai mulki ko kana kusa da gwamnati, idan ka yi cin hanci babu abin da zai faru.

Ya ce shugaba Buhari ya nuna wa 'yan Nijeriya cewa ko da ɗansa ko amininsa ne ya kauce wa hanya ta fuskar cin hanci da rashawa zai yi maganinsa.

A baya dai, majalisar dattijan Nijeriya ta buƙaci shugaba Buhari ya ɗauki mataki a kan sakataren gwamnatin nasa, amma sai ɓangaren zartarwar ya yi biris.

Har ma ya aika da wata takarda da ke nuna cewa Babachir Lawal ba shi da wani laifi kuma gwamnati ta wanke shi daga zargin da aka yi masa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Buhari ya nuna wa 'yan Nijeriya cewa ko da ɗansa ko amininsa ne ya kauce wa hanya ta fuskar cin hanci da rashawa zai yi maganinsa

Shehu Sani ya ce da sun fito da rahoto na biyu, da an ga munin ƙazantar da aka aikata.

A cewarsa sun tuntuɓi Babban Bankin Nijeriya wanda ya ba su bayanai da asusun ajiyar da aka sanya irin waɗannan kuɗaɗe.

Sanata Shehu Sani ya ce a baya, ya zargi ɓangaren zartarwa da nuna son kai a yaƙin da cin hanci saboda a cewarsa wasu jami'an gwamnati sun fitar da takardar da ke wanke Babachir Lawal.

"Lokacin da shugaban ƙasa bai nan, su jami'an gwamnati da ke kusa da shi, sai suka je suka rubuto takarda da sunansa suka ce waɗanda suka saci waɗannan kuɗi, suka kau da waɗannan kuɗi cewa wai ya riga ya wanke su."

"Abin da ni kuma na ce ba gaskiya ba ne. Kuma da na faɗi haka, ga shi magana ta fito fili Buhari bai yarda da wannan takarda da aka rubuta ba. Shi ya sa ya ɗauki wannan mataki," in ji shi.

Shehu Sani ya ce matakin ya aika da wani saƙo na cewa duk wani jami'in gwamnatin da ya kauce hanya, za a yi maganinsa.