An tabbatar da juna-biyun Serena Williams

Serena Williams Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Serena Williams ta doke 'yar uwarta Venus a wasan karshe na Australian Open a watan Janairu

'Yar wasan tennis da ta fi samun nasara a duniya a wannan zamani Serena Williams, ta samu juna-biyu, makonni 12 bayan ta yi nasarar lashe wata babbar gasar duniya a karo na 23.

Ba'amurkiyar mai shekara 35, za ta haihu ne a bazarar wannan shekara, in ji wakilinta.

Serena Williams wacce take ta biyu a kwallon tennis a duniya, ta wallafa hotonta a shafin sada zumunta na Snapchat tare da rubutun da ke dauke da sakon " makonni 20" kafin daga baya ta goge shi.

In dai batun ya tabbata, to wannan na nufin Williams na dauke da cikin mako takwas lokacin da ta lashe gasar Melbourne.

Serena Williams ba za ta yi sauran wasannin bana ba, kasancewar dama ba ta yi wasa ba tun gasar Australian Open a watan Janairu ba, inda aka ce tana fama da ciwon gwiwa.

Serena Williams, wacce za ta sake zama ta daya a duniya a mako mai zuwa, za ta iya rike matsayinta idan ta yi wasanta na farko a cikin wata 12 bayan haihuwa.

Tsohuwar gwarzuwar ta duniya Victoria Azarenka ta haifi danta na farko a watan Disamba kuma ana sa ran za ta dawo fagen daga a karshen watan Yuli.

Ita ma 'yar wasan Belgium Kim Clijsters, ta ci gasar US Open a 2009, watanni 18 kacal bayan ta samu karuwa.

A baya-bayannan ne masu karanta labarin wasanni na shafin BBC suka zabe ta a matsayin babbar 'yar wasan tennis ta duniya.

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba