Liverpool ba za ta sayi Joe Heart ba - Klopp

Joe Hart Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Joe Hart ya yi wasa sau 30 a Torino a kakar bana

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya kawar da yiwuwar kulob ya sayi golan Ingila da Manchester City, Joe Hart.

Rahotanin sun nuna cewa kolub din na Anfied na dab da shiga yarjejeniyar fam miliyan 20 don sayan mai tsaron ragar wanda aka ba da shi aro a Torino.

Ana sa ran Joe Hart mai shekara 30, zai bar City amma a yanzu Mista Klopp ya amince da masu tsaron ragarsa Simon Mignolet da Sand Loris Karius.

Klopp ya ce ''Kwararren mai tsaron gida ne amma ba ma bukatar shi yanzu ko nan gaba.''

Joe Hart ya shaida wa BBC a watan Maris cewa ''Ba shi da wani amfani a City" kuma ba ya sa ran zai sake buga wa kungiyar wasa.

Ya koma aro a Torino na Italiya a watan Agusta bayan da kocin City Pep Guardiola ya ba shi izinin barin City.

Hart ya ce ''Idan ka san ba za ka yi nasara ba, bai da amfani ka fara yaki, musamman ma da wani mai iko kamar Pep Guardiola.''

Shi dai Guardiola ya jaddada cewa ba za su yanke shawara kan Heart ba sai karshen kakar wasa ta bana.

Labarai masu alaka