Tsohon dan wasan Ingila Ehiogu ya rasu

Ugo Ehiogu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ugo Ehiogu ya taka wa Ingila leda sau hudu

Tsohon dan wasan Ingila da Aston Villa Ugo Ehiogu ya rasu yana da shekara 44 bayan da ya gamu da bugun zuciya a filin atisayi na kulob din Tottenham a ranar Alhamis.

Wata sanarwa da Spurs ta fitar ta ce Ehiogu ya rasu ne a asibiti da sanyin safiyar ranar Juma'a.

Ehiogu, wanda shi ne kocin tawagar 'yan kasa da shekara 23 na kulob din, ya taka wa Ingila leda sau hudu.

"Babu wasu kalmomi da za su bayyana irin halin dimuwar da muka shiga," a cewar kocin da ke kula da cigaban kwallon kafa a Tottenham John McDermott.

"Ba za a iya maye gurbin da Ugo ya bari ba."

Ehiogu ya taka-leda sau 200 a Aston Villa daga shekarun 1991 and 2000 sannan ya shafe shekara bakwai a Middlesbrough.

Ya lashe gasar League Cup da Villa a 1994 da 1996, da kuma Boro a 2004.

Dan wasan na baya ya kuma murza-leda a West Brom, Leeds, Rangers da Sheffield United, kafin ya yi ritaya a 2009.

Ya fara aikin koci a Tottenham a shekarar 2014.

Labarai masu alaka

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba