South Africa: An tuhumi wani fasto da aikata lalata

Shugaban Afirka ta Kudu Jocob Zuma Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hukumomin Afirka ta Kudu sun tabbatar da cewa ana tsar da faston har zuwa ranar 3 ga watan Maris

Ana tuhumar wani fasto dan Najeriya mai suna Timothy Omotoso da laifin safarar bil-Adama da kuma laifuka biyu na aikata lalata a birnin Port Elizabeth da ke Afirka ta Kudu.

An kama Mista Omotoso ne jiya a filin jirgin sama na birnin.

An dage zaman zaman kotun zuwa ranar 3 ga watan Maris, kuma za a ci gaba da tsare shi har tsawon makwanni biyu.

Babban mai gabatar da kara na kasar Tshepo Ndwalaza ya ce: "A matsayinmu na hukumar shigar da kara muna tabbatar da cewa an bayar da umarnin ci gaba da tsare Fasto omotoso har zuwa ranar 3 ga watan Maris saboda yana neman beli".