Sabo da kudi aka kaiwa Dortmund hari ba ta'addanci ba

Borussia Dortmund Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An kai a motar Borussia Dortmund hari

'Yan sanda a Jamus sun tuhumi wani mutum da ya kai hari akan motar kulob din Borussia Dortmund.

Masu kai kara sun ce maimakon a danganta harin da ta'addanci, an danganta harin da wani dan kasuwa, da ke fatan zai samu riba idan farashin kulob ya fadi.

Sergej W mai shekara 28, na cikin otel daya da 'yan wasan kulob din a cikin wani daki dake kallon titi inda fashewar ta faru.

Mutane biyu ne suka ji raunuka bayan da bama-bamai uku suka fashe kusa da motar.

An yiwa dan wasan Spain Marc Bartra tiyata a kugunshi, yayin da wani dan sanda kuma ya ji rauni.

Bayan harin da aka kai ranar 11 ga watan Afrilu an dakatar da gasar Dortmund da Monaco zuwa washe gari, abin da ya sa magoya bayan kulob Dortmund suka taimakawa wadanda ba su da wurin kwana.

Da farko 'yan sanda sun ce 'yan ta'adda ne suka kai harin, bayan da suka samu wasu wasika a wajen, wacce ke nuna cewa kungiyar IS ta kai harina.

Amma bayan mako daya , suka ga harin bashi da wata alaka da ta'addanci.

Labarai masu alaka

Karin bayani