Zakarun Turai: Real Madrid da Atletico Madrid, Monaco da Juventus

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Real Madrid ta doke Atletico Madrid a wasan karshe na gasar bara

Real Madrid za ta kara da Atletico Madrid a zagayen kusa da na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai, yayin da Juventus za ta kece raini da Monaco.

Madrid na kokarin zama ta farko da za ta kare kambunta a gasar zakarun turai a lokacin da za a buga wasan karshe ranar 3 ga watan Yuni a birnin Cardiff.

Shi kuma kulub din Monaco na Faransa zai kece raini da Junventus na Italiya a daya wasan.

Za a yi karawar farko ranar 2 da 3 ga watan Mayu, sannan kuma kungiyoyin su sake kece raini a makon da ke biye.

Real Madrid dai wacce ke fatan lashe gasar zakarun turai karo na 12, ta doke zakarun Jamus Beyern Munich 6-3 jumulla.

Ita kuma a nata bangaren, Atletico ta kawo matakin ne bayan doke Leceister da ci 2-1 jumulla.

A bangare daya kuma Juventus ta lallasa Bercelona 3-0 a karawar da suka yi daban-daban, yayin da Monaco ta doke Borussia Dortumund 6-3.

A gasar Europa League kuma, Manchester United za ta kara da Celta Vigo yayin da Ajax za ta kece raini da Lyon.