Europa League: Ko Man Utd za ta iya doke Celta Vigo?

Manchester United Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Marcus Rashford ya taimaki Manchester United wurin kai wa wannan mataki

Manchester United za ta kara da Celta Vigo a wasan zagayen kusa da na karshe na gasar Europa League.

United ta taba lashe gasar zakarun Turai sau uku amma ba ta taba nasara a gasar ta Europa ba.

Kungiyar Ajax da Holland da ta lashe gasar a shekarar 1992 za ta kara da Lyon na Faransa.

Za a buga wasannin farko a ranar 4 ga watan Mayu da na biyu kuma a rana 11 ga watan na Mayu.

Kocin United Jose Mourinho ya lashe gasar a lokacin da yake tare da Porto a shekarar 2003 kuma zai kara da Celta, da dasu taba lashe wata babbar gasar Turai ba.

A gasar zakarun Turai, Real Madrid za ta kara da Atletico Madrid, sai Monaco da za ta kece raini da Juventus.

Labarai masu alaka