Wasannin Premier da aka buga ranar Asabar

premier Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ko sau daya, Everton ba ta kai hari mai kyau ba a wasan

Kungiyar kwallon kafa ta Everton ta kuskure damar zama cikin kungiyoyi biyar dake kan gaba da teburin gasar Premier ta Ingila, bayan da ta tashi babu ci a fafatawar da ta yi da West Ham ranar Asabar.

Wasan yafi yi wa Manajan West Ham, Slaven Bilic kyau, domin mai daya samu ya kara daga kubol din sama a teburin gasar, inda yanzu tazarar maki 7 ne tsakanin kulob din da Swansea.

Kulob din Swansea kuwa ya na fatan ganin bai fice daga gasar Premier ba, yayin da ya doke Stoke City da 2-0.

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Fernando Llorente ne ya fara ci Swansea kwallo da kai

Fernando Llorente ne ya fara ci wa Swansea kwallo, sannan Tom Carroll ya ci ta biyu daga tazara mai dan nisa.

Har yanzu Swansea ce ke mataki na 18 a teburin gasar.

Ita kuwa kungiyar Middlesbrough, fatan da take da shi na kaucewa fitacewa daga gasar Premier ne ya sake gamuwa da cikas, bayan da ta sha kashi a hannun Bournemouth da ci 4-0.

Middlesbrough na mataki na 19 a teburin gasar.

Kulob din Hull City kuma ya samu nararar doke Watford da ci 2-0, duk da cewa yayi wasanne da 'yan wasa 10.