Kwallon Martial ta jawo wa Man Utd biyan karin fam miliyan 8

Anthony Martial a yayin da yake zura kwallo ragar Burnley Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Anthony Martial ya ci wa Manchester United kwallo ta takwas a bana

Manchester United ta ci gaba da fafutukar neman gurbin kungiyoyi hudu na gaba a teburin Premier bayan da ta bi Burnley har gida ta doke ta 2-0, ranar Lahadi.

Anthony Martial ne ya fara daga ragar masu masaukin bakin a minti na 21, wadda ita ce kwallo ta 25 da ya ci wa United, kuma sakamakonta Manchester za ta cika wata yarjejeniya ta sayen dan wasan dan Faransa, inda za ta biya tsohuwar kungiyarsa Monaco, karin fan miliyan takwas da rabi.

Wayne Rooney wanda wannan shi ne karo na biyu a wasan Premier da ake sa shi a farkon wasa a shekarar nan, shi ne ya ci kwallo ta biyu a minti na 39.

Nasarar ta sa United ta ci gaba da zama ta biyar a tebur, amma kuma maki daya ne tsakaninta da abokiyar hamayyarta Man City ta hudu mai maki 64, wadda kuma za su kara ranar Alhamis a Etihad.

Kyaftin din na Ingila wanda ya taka rawa sosai a wasan, ya kasance daya daga cikin sauyi takwas da kociyansu Jose Mourinho ya yi bayan nasarar da suka yi a wasan Kofin Europa da suka buge Anderlecht ranar Alhamis, bayan raunin da Zlatan Ibrahimovic da dan wasan baya Marcos Rojo suka ji.

Ita kuwa Burnley har yanzu wasa 11 kawai ta ci, kuma maki biyar ne tsakaninta da rukunin faduwa daga gasar ta Premier, inda take matsayi na 15.