Wenger ya kalubalanci 'yan wasan Arsenal 'yan Birtaniya

Arsene Wenger na magana da daya daga cikin 'yan wasansa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Arsenal ta dauki kofin FA shida tare da Wenger

Kociyan Arsenal Arsene Wenger ya kalubalanci 'yan wasan kungiyar 'yan asalin Birtaniya da su dauki nauyin makomar kungiyar.

Wenger ya ce abin zai fi dacewa ga 'yan wasa 'yan gida, kamar su Ramsey da Chamberlain, saboda a Arsenal aka rene su.

Duk da cewa kociyan dan Faransa har yanzu bai sanar ko zai sabunta kwantiraginsa ya ci gaba da aiki har karshen wannan kakar ba, ya yi amanna a tsarin da ya gina kungiyar tsawon shekara 20 za ta dore haka ko ba shi.

Wenger ya ce dole ne 'yan wasan su karbi ragamarta, su ce ga yadda suke son su yi, ga yadda suke son su yi wasa tare.

Kociyan ya ce in kuma ba sa son hakan, to lalle lamarin zai kasance babban abin takaici.

Wenger ya kalubalanci 'yan wasan nasa ne kafin wasansu na kusa da karshe na Kofin FA na ranar Lahadi da Manchester City, wanda zai iya kasancewa lokaci na karshe da kociyan zai jagoranci kungiyar zuwa Wembley.

Haka kuma wasan shi ne karo na 11 da yake kai kungiyar wannan mataki na kusa da karshe na kofin, wadda kuma ita ce dama ta karshe ta daukar wani kofi a bana.