Lazio ta kafa tarihin saurin ruwan kwallaye a Serie A

Ciro Immobile lokacin da yake zuwa kwallo ragar Palermo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ciro Immobile ya zura kwallo a minti na 8 da na 9

Lazio ta zama kungiya ta farko da ta ci kwallo biyar a cikin minti 26 da fara wasa a gasar Serie A ta Italiya tun 1938, bayan da ta lallasa Palermo wadda ke neman tsira, 6-2.

Kungiyar wadda sakamakon nasarar ta zama ta hudu a tebur da maki 64, tana kan gaba ne a wasan da kwallo 2-0, da Ciro Immobile ya ci a cikin minti 10.

Daga nan ne kuma sai Keita Balde Diao ya rika daga ragar Palermon dai-dai, har sau uku rigis, tsakanin minti 21 da minti 26, kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne Andrea Rispoli ya ci wa Palermo biyu kafin Luca Crecco ya ci wa Lazio ta shida a mintin karshe na wasan..

Kungiya daya da ta taba cin kwallo biyar cikin dan takaitaccen lokaci haka a gasar ta Serie A, ita ce Juventus, wadda cikin minti 21 ta zura wa Fiorentina kwallo biyar, a wasan da suka tashi 5-2 shekara 79 da ta wuce.

Ga sakamakon sauran wasannin na Serie A na ranar Lahadi:

Sassuolo 2-2 Napoli

Chievo 1-3 Torino

Milan 1-2 Empoli

Sampdoria 1-2 Crotone

Udinese 2-1 Cagliari